23 Maris 2016 - 18:51
Yahudawan Isra'ila Na Ci Gaba Da Mayar Da Martani Kan Jawabin Sayyid Nasrullah

Kalaman da jagoran kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya yi dangane da martanin da kungiyar za ta mayar kan Isra'ila matukar dai ta sake kai wani hari kan Lebanon, ya kawo martani daga yahudawan Isra'ila

Tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, bayan zantawar da ta yi da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah a daren Litinin da ta gabata, yahudawan Isra'ila suke ci gaba da bayyana firgicinsu kan barazanar da ya yi.

Masana da masu sharhi a Isra'ila, sun bayyana a kafofin yada labarai suna bayyana barazanar da Sayyid Nasrullah ya yi kan tarwatsa duk wasu muhimman wurare a kowane sako na Isra'ila, matukar ta kai hari a Lebanon da cewa, abin da ya fada da gaske ne, kuma Hizbullah tana da karfin da za ta yi hakan a halin yanzu, lamarin da ya jefa firgici da tsoro a cikin zukatan yahudawan Isra'ila maras misiltuwa.288